Kamfanonin sun shigo da shinkafa da ya kamata su biya harajin da ya kai nera miliyan dubu dari ashirin da bakwai.
Shugaban hukumar kwastan yace kamfani hudun sun wuce adadin shinkafar da aka basu izinin shigowa da ita da ninki goma. Yakamata su biya haraji akan adadin kayan da suka shigo dashi amma basu yi ba duk da cewa sauran kamfanonin sun biya nasu harajin..
Tun farko shugaban kwastan ya rubutawa gwamnatin da ta shude cewa a sa kamfanonin su biya. Har ma ya rufe gidajen ajiyar kayan sai aka sa ya budesu.
Ya basu lokaci su biya duk da cewa an rage masu haraji amma kuma suka ki. Abun takaici yawancin masu kamfanonin ba 'yan Najeriya ba ne.
Yanzu dai an rufe kamfanonin har sai sun biya harajin dake kansu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5