Hukumar Kwastam Ta Yi Ikrarin Tara Biliyoyin Naira

Hukumar kwastam dake kula da tashar jiragen ruwan unguwar Apapa a birnin Legas ta sami kudin shiga na fiye da Naira biliyan 400, da kuma Naira biliyan 73 daga harajin kayayyakin da ake fitarwa da kuma shigo da su Najeriya a shekarar da ta shude.

Babban kwanturolan hukumar ta kwastam mai kula da tashar jiragen ruwan Apapa, Alhaji Bashir Abubakar, shi ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka yi a birnin Legas, ya ce wadannan kudaden da hukumar ta tara zasu taimakawa gwamnati, maimakon dogaro da man fetur da kasar ke yi domin samun kudaden shiga.

Alhaji Bashir ya ce yanzu haka akwai kwantenoni fiye da 1,300 da aka kama a wannan tashar kuma tuni suka gabatar da rahoto ga shugaban su Kanal Hameed Ali, ciki kuwa har da wasu masu dauke da kwayar Tramol da yace sun kama akwati 41, koda yake ba dukan kwantenonin ke da kayan fasa kwauri ba. Ya kuma ce sun kasa sun tsare suna jira su ga wanene zai zo yace nashi ne.

Yanzu dai a yayin da kakar zabe ta kankama, hukumar ta baza jami’an ta domin sa ido akan shigowa cikin Najeriya da makamai da kayan jami’an tsaro da wasu ka iya amfani dasu domin tada husuma a cikin kasa a cewar Kwanturolla Bashir Abubakar.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kwastam Tace Ta Tara Kudi Masu Yawa A Shekarar Da Ta Wuce - 3'19"