Hukumar Kwallon Kafar Algeriya Ta Dauki Hayar Marseille A Matsayin Sabon Koci

Hukumar dake kula da wasan kwallon kafa ta kasar Algeriya ta bayyana sunan sabon mai horar da kungiyar kasar kuma tsohon dan wasan kwallon kafa na Marseille dake kasar Faransa mai suna Djamel Belmadi a matsayin sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar.

Sabon Kocin Belmadi, shine ya maye gurbin tsohon Kocin Algeriya kuma tsohon dan wasan kasar mai suna Rabah Madjer.

Belmadi, mai shekaru 42 da haihuwa ya samu nasarar haskakawa a yayinda yake buga wasa aa kulob din Marseille, na kasar Faransa daga shekara ta 2000 zuwa 2003.

Ku Duba Wannan Ma Zakarun Da Za Su Kara a Neman Lambar Yabo Ta Ballon d'Or

Kocin ya rataba hannu a yarjejeniyar kwantiragin shekaru hudu da kungiyar kwallon kafa ta kasar Algeriya, inda yake da babban aikin dake gabansan na samawa kasar ta Algeriya, nasarar samun tikitin shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta Nahiyar Afrika, a shekara ta 2019, wanda za'ayi a kasar Kamaru, da kuma gasar cin kofin Duniya a can Qatar a shekara ta 2022.

Kwac Belmadi, ya taba jagorantar kungiyar kwallon kafar ta Qatar na tsawon shekara daya a 2014. Hukumar kasar ta yi masa fatan alheri a yayinda yake jagorancin kasar ta Algeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kwallon Kafar Algeriya ta Dauki Hayar Marseille A Matsayin Sabon Koci 2' 20"