Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta mika gaisuwar ta’aziyyar ta ga tsohon kocin ‘yan wasan kasar Stephen Keshi, bisa rasuwar matar sa mai suna Kate, wadda ta rasu a jiya laraba.
Shugaban hukumar Amaju Pinnick ya dauki lokaci yana tattaunawa da tsohon kocin ta wayar tarho a yau alhamis a yayin da labarin rasuwar yake cigaba da yaduwa.
Majiyoyi sun bayyana cewa marigayiyar ta rasu ne jiya ranar laraba a kasar Amurka bayan gajeruwar rashin lafiya.
Amaju Pinnick ya ce “lallai wannan babban rashi ne kuma abin damuwa kwarai, domin kuwa rasa mata ba karamin abu ne mai taba zuciya ba, muna addu’ar ubangiji ya bada hakuri, kuma yayi maka da iyalinka ta’aziyya”.
Tsohon kocin dai ya rike mukamin kyaftin na kungiyar ‘yan wasan Najeria sama da shekaru goma, kuma a lokacin sa, kungiyar ta sami kyautar zinari na wasan cin kofin kasashen Afirka, da azurfa da tagulla, ya kuma jagoranci kungiyar kwallon kafar har ya zuwa lokacin da kungiyar ta sake yin fice karo na uku a Afirka ta kudu a shekarar 2013.
Keshi ya kasance babban kocin kungiyar ‘yan wasan super eagles tsakanin shekarar 2011 da 2015 a yayin da kungiyar ta kai zagaye na 16 a watan Yuni, a wasan cin kofin duniya na hukumar FIFA a Brazil.