Hukumar Kula Da Wasannin FA Za Tayi Kwaskwarima

Hukumar da take kula da wasan kwallon kafa ta kasar Ingila FA, ta fara tattaunawa domin kawo wasu sauye sauye a gasar da akeyi a kasar, ciki har da tafiya hutu a watan Janairu, kamar yadda sauran kasashen nahiyar Turai su keyi domin samun hutawa.

Matakin da hukumar ta dauka ya samo asaline sakamakon korafe korafe da akayi, ta kawo mata daga bangaren masu horaswa da kuma masu sharhi a kan harkokin kwallon kafa ta duniya.

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Enesto Valverdes ya taba korafin cewa gasar firimiya tana da wahala sosai duba da rashin hutu, yace ya kamata a dinga samun hutu ko da na sati biyu ne.

Canje canjen sun hada da buga wasa daya tak a gasar cin kofin kalu bale FA CUP na kasar koda ya kasance anyi canjaras maimakon ace sai an koma gidan wanda yayi wasan farko a waje, hakan yana nufin za’ayi bugun daga kai sai mai tsaron gida wato (Penalties).

Hukumar tace zata duba batun maganar dawo da yin wasa daya tilo a wasan kusa dana karshe na cin kofin Carabao Cup maimakon shima wasa biyu da ake bugawa gida da waje.

Hukumar zatayi zama dan tautaunawa kan sababbin canje canje tare da masu gudanar na kungiyar masu horaswa na gasar, da kuma shugabannin
kungiyoyi a karshen wannan watan na Afirilu a kasar ta Ingila domin tabbatar da canje canjen a hukumance.