Hukumar Kokawa Ta Jamhuriyar Niger Ta Shiga Rikicin Shugabanci

Wasan kokawa a Jamhuriyar Niger

A taron manyan hukumar kokawa ta jamhuriyar Niger da suka zauna a Zinder suka yanke shawarar tsige shugabanta, Alhaji Abuba Ganda tare da nada shugaban riko nan take har sai an gudanar da wani zabe.

An zargi Abuba Ganda da yin wasu kalamun da ak ce basu dace da shugabanci dalili ke nan da suka dakatar dashi daga shugabanci.

To sai dai wani taron da aka gudanar a Birnin Yamai ya sake mayar da Alhaji Abuba Ganda kan kujerarsa, ke nan an samu shugabanni biyu.

Wani bangaren hukumar a karkashin shugabancin Alhaji Adamu Haruna Hassan na yankin Agadez ya sake jaddada dakatar da shi Alhaji Abuba Ganda.

A martini da ya mayar akan dakatar dashi, Alhaji Abuba Gand, ya ce shi kam yana nan daram dam akan kujerarsa yana mai cewa babu wanda ya kirashi ya fada mashi laifinsa, kazalika babu wanda ya rubuta masa ya sanar dashi an dakatar dashi.

Sai dai an danka shugabancin hukumar hannun wani tsohon dan kokawa Ali Dan Malam domin rikon kwarya. Ya kuma bada tabbacin cewa rikicin ba zai shafi gasar wasan da aka shirya yi a Damagaran ba.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kokawa Ta Jamhuriyar Niger Ta Shiga Rikicin Shugabanci - 3' 03"