Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya Ta Jaddada a Kare Kananan Yara ‘Yan Kasa da Shekaru Biyar Daga Rasa Rayukansu Sakamakon Wasu Cututtuka

Taron kasashe biyar na Afirka da suka fi fama da cutar zazzabin cizon sauro ko malaria a Abujan Najriya

A taron kasashen Afirka biyar da suka fi fama da cutar zazzabin cizon sauro ko malaria da aka yi a Abujan Najeriya, Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya, WHO, ta jaddada bukatar a kula da yara ýan kasa da shekaru biyar daga rasa rayukansu sanadiyar wasu cututtukan da ana iya kauce masu ko warkar dasu idan aka dauki matakan da suka dace cikin gaggawa

Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya, WHO, ta karfafa bukatar kula da yara kanana ‘yan kasa da shekaru biyar daga rasa rayukansa sakamakon wasu cututtuka, wadanda ake iya magancewa kafin su yi wani illa, kamar zazzabin cizon sauro, sharkewar nunfashi da kuma amai da gudawa.

A wajen taron kasashe biyar da suka fi fama da cutar zazzabin cizon sauro da aka yi a Abujan Najeriya ne hukumar ta yi wannan gargadin. Kasashe biyar din sun hada da Najeriya, Nijar, Jamhuriyar Dimokradiyar Congo, Malawi da Mozambique.

Hukumar Kiwon Lafiyar ta kalubalanci hukumomin kasashen su himmatu wajen wayar da kan iyaye a yankunan karkara, su koyi yadda zasu ba da taimakon gaggawa ga yara.

Muhammad Musa Abubakar, jami’in kiwon lafiya a matakin farko daga Najeriya, ya ce akwai hadin kai da hadin gwiwa da ake yi da WHO da kasashe domin tabbatar da inganta kiwon lafiyar yara.

Muhammad Musa Abubakar a taron kasashe biyar dake fama da cutar malaria, kuma jami'in kiwon lafiya matakin farko a Najeriya

Daya daga cikin jami’an kungiyoyin kiwon lafiya da suka halarci taron, Jibril Labbo, ya ce saka iyaye cikin yekuwar nada mahimmanci domin su ne suke tare da yara dare da rana, sannan kuma yin hakan zai rage yawan mace-macen yara.

Nasiru Adamu El-Hikaya na da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya Ta Jaddada a Kare Kananan Yara ‘Yan Kasa da Shekaru Biyar Daga Rasa Rayukansu Sakamakon Wasu Cututtuka - 2' 56"