"Dole 'Yan Kasuwa Su Rage Cin Kazamin Riba" - Hukumar FCCPC

Kasuwa a Najeriya

Hukumar da ke kula da gasa da kare muradun masu amfani kaya ta tarayya (FCCPC), ta ba da wa’adin wata guda ga ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a kasuwannin da ke kara kazamin riba kan kaya da su rage tsadar farashin kayayyakin na su ko doka ta yi aiki kan su.

Sabon mataimakin shugaban hukumar ta FCCPC da aka nada, Mr. Tunji Bello, shi ne ya bayyana haka a wani taron wuni guda da masu ruwa da tsaki kan sayar da kaya da tsada a ranar Alhamis a Abuja.

Wata kasuwa a Garki Area 11

A cewar Bello, hukumar za ta fara karfafa wannan umarnin bayan wa’adin da aka ba su.

Ya ce an yi taron ne domin magance karuwar hauhawar farashin kayayyakin masarufi da tsadar farashin ayyuka da kuma munanan dabi’un kungiyoyin ‘yan kasuwa.

Bello ya bayyana sakamakon wani binciken da hukumar ta gano cewa ana sayar da wani karamin injin markade sanfurin Ninja a wani babban kanti a jihar Texas ta Amurka akan kudi dala 89 (N140,000.00) amma ana sayar da samfurin akan N944,999.00 a wani babban kanti dake Victoria Island, Legas.

Kasuwa

Bello ya yi al’ajabin dalilin farashin injin ya yi tashin gwauron zabi idan aka kwatanta da farashin a Texas ta kasar Amurka.

Ya ce irin wa’dannan munanan dabi’u da kayyade farashi na barazana ga bunkasar tattalin arzikin kasar.

“A karkashin sashen doka na 155, masu karya dokar farashi ko dai daidaikun mutane ko kuma kamfanoni na fuskantar hukunci mai tsanani da ya hada da tara da dauri idan kotu ta same su da laifi.

Kasuwa

“Manufar wannan mataki ita ce hana duk wani bangare da ke da hannu a irin wannan haramtaccen aiki. Koda yake, tsarinmu a yau ba na hukunci ba ne. Don haka ina kira ga masu ruwa da tsaki da su rungumi kishin kasa da hadin kai.

-Punch-