Hukumar Majalisar dinkin duniya mai kula da kare hakkin bil–Adam, ta jinjinawa hukumar kare hakkin bil-Adam ta kasar Nijar, a kasancewarta na kaiwa matakin sahun farko a jerin kasashen duniya dake fafutukar kare hakkin bil–Adam.
WASHINGTON, DC —
Wannan mataki da kungiyar ta samu zai bata damar yin jawabi a gaban majalisar dinkin duniya kamar yadda gwamnatin kasar Nijar zata iya yin jawabi a gaban hukumar kuma tana iya tsayawa takara a duk wani mukami a hukumance da ya shafi fafutukar hakkin bil-Adam.
Suma kungiyoyin dake kare hakkin bil-Adam, na jamhuriyar Nijar sun tabbatar da cewa rashin yin kasa a guiwa ne ya bata damar samun wanna matsayi kamar yadda daya daga cikin masu fafutuka akan kare hakkin bil-Adam, Malam, Jiboce Mago ya furta.
Yakar da cewa da wanna matsayi da hukumar ta samu wani nauyi ya sake hawa kanta na ganin cewa ta kara jajirce wajen kare hakkin bil-Adam, aninda yake dama shi take yi.
Your browser doesn’t support HTML5