Hisbah na Cigaba da Binciken Samarin da ta Kama Su na Kokarin Auren Juna

Wani dan Daudu. (File Photo)

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, tace tana cigaba da bincike akan wasu matasa samari 12 da jami’anta suka kama a ranar Lahadin data gabata bisa zarginsu dayin ayyukan daudu da kuma yunkurin kulla aure a tsakaninsu.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, tace tana cigaba da bincike akan wasu matasa samari 12 da jami’anta suka kama a ranar Lahadin data gabata bisa zarginsu dayin ayyukan daudu da kuma yunkurin kulla aure a tsakaninsu, lamarin daya saba da tanade-tanaden dokar jihar Kano ta hana ayyuka daudu da karuwanci da kuma dukkkanin abubuwa masu nasaba dasu.

Babban aikin hukumar Hisbah dai shine umarni da kyawawan ayyuka dakuma hani da mummuna.

A ranar Lahadin data gabatane jami’an hukumar ta Hisba a jihar Kano, suka kama wadansu samari matasa a wani lambun shakatawa da gudanar da bukukuwa dake wajen birnin Kano, kan titin zuwa Zariya. Samarin dai ana zarginsune da yin aikin daudu dama yinkurin kulla aure a tsakaninsu, lamarin da yaci karo da shari’ar musulunci da kuma dokar gwamnatin tarayya wadda shugaba Goodluck Jonathan ya sanyawa hannu. Wakilinmu Muhmud Ibrahim Kwari, yayi hira da darakta janal na hukumar Hisbah Mallam Abba Sa’idu Sufi, inda ya tambayeshi cewar,ko yanzu a wanne hali matasan ke ciki bayan jami’an hukumar Hisbah suka kamesu? Mallam Sa’idu Sufi, yace, “to wadannan guri da aka kama wadannan matasa, kuma jihar Kano jihace ta shari’ar musulunci a kwai doka, wadda ake cewa da ita dokar hana karuwanci da sauran fasadi a fadin jihar Kano. Wanda yake ita wannan al’ada ta daudu wato mutum ya koma ya dinga alakanta kansa da mace, sa kaya, rangwada dama magana irin ta mata, to tabbas yin hakan ya sabi addinin musulunci.”

Saurari hirar Muhmud Ibrahim Kwari da Mallam Abba Sa’idu Sufi, domin jin cikakkiyar tattaunawar su.