Kusan agoguna guda 50 aka kwace daga hannun wasu jami’an kwallon kafa wandanda suka karba a matsayin kyauta gabanin gasar kwallon kafa ta duniya a kasar Brazil aka kuma kyautar da su ga kungiyoyin kwallayen kafar wadanda ke amfani da kwallo wajen taimakon matasa.
Kiyasin kudin agogo daya daga cikin agogunan ya kai kimar kudin kasar Siwizalan 25000 daidai da dalar Amurka 24,400 ko kudin tarayyar Turai na Euro 23,000.
Kwamitin tabbatar da da’ar aikin na hukumar FIFA ne suka bayar da kyautar agogunan da aka bawa ma’aikatan wanda suke kallo a wani salon cin hanci a fakaice.
Hukumar kwallon kafa ta kasar Brazil ce ta mikawa FIFA wasu jakunkuna har guda 65 kunshe da agogunan samfurin kirar Parmigiani da aka bawa jami’an kasashen da ke gasar kwallon guda 32.
Wanna kyauta dai ta kawo kace-nace a duniyar kwallon kafa tare da yarfawa ko kunyata jami’an FIFA ciki har da shugaban hukumar Sepp Blatter wanda ya musanta wannan zargi na karbar cin hanci.