Hukumar EFCC Tayi Nasara A Kotu

EFCC

Da Alamun cewa an kama hanyar mallakawa Gwamnatin Najeriya kudaden da hukumar EFCC ta kama

A karon farko wata kotun Najeriya ta mallakawa Gwamnatin kasarmiliyoyin Naira da hukumar EFCC ta kama a Lagos, hukuncin da ake ganin ya kama hanyar mallakawa Gwamnati duku wasu kudade da hukumar EFCC zata kama anan gaba muddin dai aka kasa samun wanda ya mallaki kudaden da EFCC ke kamawa.

Wannan hukunci da babbar kotun Najeriya dake Lagos, ta zartar dai ya kasance na farko da wata kotu ta fara zartarwa akan kudaden da hukumar EFCC, ta kwace daga hannun wasu ‘yan kasar da ake kyautata zaton cewa kudaden an sanesu ne ta haramtattun hanyoyi kimanin Naira milyan dari biyar ne dai hukumar ta EFCC ta kama a watan Afrilun wannan shekara inda kuma ta gabatar da kudin ga kotun tarayyar Najeriya dake Lagos, domin neman kotu ta mallakawa Gwamnatin tarayya kudaden.

A hukuncin da Justice Rilwanu Aikawa, ya zartar wa bada hukuncin wucin gadi na makoni biyu da kuma bukatar hukumar ta EFCC, da ta gabatar da tallace tallace a wasu jaridun Najeriya dake cigiyar wadannan kudade da aka gano.

Sai baya cikar wa’adin na makoni biyu babu wani da ya gabatar da kansa a matsayin wanda ya mallaki wadannan kudade ciki kuwa harda wani mai suna Muhammad Tauheed, da hukumar EFCC ta gabatar da sunan sa a matsayin mai mallakar shagon da ake musayan kudade a cikinsa inda kuma anan aka gano kudaden.

A hanzarin da ya gabatar a gabn kotu lauyan hukumar EFCC, Idris Muhammad, yace bias doka tunda wa’adin da kotu ta bayar ya cika batare da waniya gabatar da kansa a matsayin wanda ya mallaki wadannan kudade ba kamata yayi kotu ta mallakawa Gwamnatin tarayya, batare da bata wani lokaci ba alkalin koyun Justice Rilwan Aikawa, ya amince da bukatar lauyan na EFCC, inda ya mallakawa Gwamnatin tarayya kudaden Naira miliyan dari hudu da arba’in da tara da digo shida.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar EFCC Tayi Nasara A Kotu - 4'07"