Hukumar EFCC Ta Soma Binciken Babban Daraktan Hukumar Leken Asirin Kasa da Aka Kora Daga Aiki

EFCC

Yanzu dai a fili take cewa batun badakalar da ta sa aka kori Ambassador Ayo Oke, tsohon babban daraktan hukumar leken asirin kasa, bai mutu ba saboda hukumar EFCC ta fara bincikensa da nufin gurfanar dashi gaban kuliya

Har yanzu dalilin korar babban shugaban hukumar leken asirin kasa, Ambassador Oke, daga aiki bai kare ba domin hukumar EFCC ta fara binciken dalilin da ya sa aka koreshi da Babachir Lawal daga aiki.

Barrister Mainasara Umar kwararre akan kundun tsarin mulkin Najeriya ya bayyana ma’anar binciken. Kafin EFCC ta fara bincike sai shugaban kasa ya fitar da sakamakon binciken da ya sa a yi a kansu. Tun da EFCC ta fara binciken, ke nan shugaban kasa ya fitar da sakamakon binciken da aka yi masa a kan mutanen biyu.

Halima Baba Ahmed gimbiyar fafutikar kare hakkin mata da yara na ganin binciken da EFCC ta fatra yi, alama ce da ta nuna yanzu an fara daukan matakin kai ga mutanen da ake ganin ba sa tabuwa.

Amma Deji Adeyanju na kungiyar Concerned Nigerians na ganin har yanzu da sauran rina a kaba saboda wai bai kamata shugaban kasa ya yi sako-sako da daukan matakin ladaptarwa ba akan wadanda suke kusa dashi. Ya ce yadda aka dauki mataki akan Ambassador Oke, ya kamata a kai kan Babachir Lawal da Abba Kyari da Maikanti Baru da dai sauransu da ake zargi da cin hanci da rashawa ko yin zarmiya

To saidai Dr Garba Abari shugaban hukumar wayar da kawunan al’umma ya ce da ma gwamnati tana yaki da cin hanci da rashawa ta hanyoyin da za’a samu zaman lafiya ne.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar EFCC Ta Soma Binciken Babban Daraktan Hukumar Leken Asirin Kasa da Aka Kora Daga Aiki - 3' 17"