Hukumar EFCC Ta Karbi Duba Asusun Hukumar Leken Asiri Ta NIA

EFCC

Gwamnatin Najeriya ta bada tabbacin hukumta duk wanda yake da hannu game da kudaden da hukumar EFCC ta gano a wani gida a Ikoyi cikin Legas wanda hukumar kelen asiri ta NIA tace nata ne na gudanar da ayyukanta.

Tuni dai gwamnati ta dakatar da shugaban hukumar leken asirin Mr. Ayo Oke kuma ya fuskanci bincike daga kwamitin da shugaban kasa ya kafa a karkashin mataimakinsa.

Kudaden kimanin dalar Amurka miliyan arba'in da uku an ganosu ne a wani gida dake Ikoyi cikin birnin Legas wanda daga bisani aka gano cewa gidan na matar Mr. Ayo Oke ne shugaban hukumar

Jaridar yanar gizo ta Premium Times ta bada labarin cewa a halin yanzu hukumar EFCC ta karbi duba asusun hukumar ta NIA cikin binciken da ake gudanarwa.

Kakakin Shugaba Buhari, Garba Shehu yace gwamnatin Buhari ba zata boye duk wani mai laifi ba. Yana mai cewa abun da zai biyo baya shugaban kasa ne zai fada idan ya ga rahoton. Amma, a cewarsa a daina yiwa shugaban kallon hadarin kaka domin duk abun da ya dace yana kuma bisa shari'a zai dauka akan kowa yake da hannu cikin wannan badakalar.

Tsoffin jam'an Najeriya da suka hada da tsofon ministan hakokin waje Farfasa Bolaji Akinyemi da kuma tsofon hukumar kasashen da Birtaniya ta yiwa mulkin mallaka Emeka Anyaokwu sun bayyana illar binciken hukumar ta NIA daga wajen hukumar domin muradun tsaron Najeriya.

To saidai shahararren dan jam'iyyar PDP da ya canza sheka zuwa APC Lamido Chikere yace rashin binciken ne illar saboda yakin da shugaban kasa Buhari yake yi bashi da magoya baya walau daga wadanda suke kusa dashi ko wadanda suke nesa dashi.

Injishi indan an zabi shugaba nagari to yakamata a samu mataimaki nagari kada ya zama jeka na yika. Haka ma wadanda suke aiki da shugaban su zama masu adalci kada su kasance masu yiwa tattalin arziki zagon kasa.

Yanzu dai jinyar da Shugaba Buhari ya keyi a Ingila ta sanya jinkiri akan fitar da sakamakon binciken Ayo Oke da sakataren gwamnati David Babachir Lawan.

Amma tuni Sanata Shehu Sani a Majalisar Dattawa ya karanta rahoton samun sakataren da laifi. Yace a cikin kudi N13bn da gwamnatin tarayya ta sakan ma kwamitin taimakawa 'yan gudun hijira an yi almubazaranci na fiye da N8bn. Mafi yawan kwangilar da aka dinga bayarwa, jami'an gwamnati ne suka dinga ba kansu da 'yanuwansu.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumae EFCC Ta Karbi Duba Asusun Hukumar Leken Asiri Ta NIA - 2' 59"