Hukumar EFCC a Gombe Tayi Gargadi Akan Magudin Zabe

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya ta gargadi ‘yan siyasa da ma duk masu alaka da hidimar zabe da su kauracewa duk wani nau’in almundahana a yayin gudanar da zaben gama gari da za a yi ranar Asabar 16 ga watan nan na Fabarairu.

Hukumar tayi wannan gargadin ne a wani taron manema labarai da ta kira a jihar Gombe, helkwatar hukumar a shiyyar.

A wata tattaunawa da jami’in hulda da jama’a na hukumar EFCC shiyyar arewa maso gabas, Malam Bello Bajoga yayi da wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammed, yayi karin haske game da irin shirin da hukumar ta yi.

Sai dai kuma a yayin da hukumar ta EFCC ke jan kunnuwan jama’a, a daya gefen kuma kungiyoyi dabam dabam na al’umma suna gudanar da tarurruka domin bayyana goyon bayansu ga ‘yan takara.

Sakataren kungiyar makafi na kasa, Musa Nuhu ya bayyana cewa sun yi wani taro a birnin tarayya Abuja kuma sun yanke shawara akan wanda zasu zaba.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar EFCC a Gombe Tayi Gargadi Akan Magudin Zabe - 1'43"