Jihohin dake shiyyar Arewa Maso Gabas din kuwa sune , Jihar Adamawa,Bauchi,Borno, Gombe, Taraba, dakuma jihar Yobe.Wakilin hukumar bunkasa Shiyyar Arewa Maso Gabas,wanda shine shugaban sashen Muhalli da Albarkatun Gona, a hukumar, Malam Adamu Lawan, ya bayyana gamsuwarsa da abin daya gani, sannan ya shaida cewa, za’a fadada shirin nan gaba domin samar wa matasan shiyyar aikin dogaro dakai.
Shugaban Bangaren Kula da Muhalla da Tattalin Ma'adanai a hukumar, Adamu Lawan, ya ce abin ya burge shi. “gaskiya nayi farin ciki da abunda na gani cewa sun yi murhu wanda muka gani wanda ya zama ginshiki ne na karfafa Arewa Maso Gabas gabadaya saboda sun samu koyarwar hanyar cin abinci kuma su koyar da wasu saboda an koyar da su don su koyar da wasu…”
Wadanda aka koya musu sana’o’in a birnin Bauchi na tsawon mako guda, sun yaba da shirin, inda su ke fatan in sun koma jihohinsu za su koyawa wasu matasan don suma su amfana daga shirin ne dogaro dakai, wanda daga nan kuma abin zai yi ta habaka, har ita kuma al'umma baki daya ta amfana.
Wani daga cikin wadanda su ka amfana ya ce, "To alhamdulillahi, babban abunda za mu yi sai godiya ga Allah da ma’aikata na hukumar cigaba ta kasa, wanda Allah ya dora mata alhakin kula da cigaban Arewa Maso Gabashin kasar. Mu abunda muka gani a wannan sati dayan, alkaluma sun nuna cewa mutanen Arewa maso Gabas ba abunda da muka rasa, dama ce kawai ba wai mun gaza ko bamu da ilimi ba ne…”
Saurari cikkaken rahoton Abdulwahab Muhammad
Your browser doesn’t support HTML5