Injiniya Abdullahi Isa sabon kwamanadan hukumar dake kula da albarkatun man fetur a jihar Neja yace sun rufe gidajen ne saboda suna sayar da man fiye da farashin da gwamnati ta kayyade.
Yace a duk fadin jihar ta Neja da wuya a samu gidan man dake sayar da fetur akan farashin da gwamnati ta tsayar. Daga Juma'a zuwa yau hukumar ta rufe gidajen mai bakwai. Yace zasu cigaba da bin gidajen man kuma duk wanda yake sayarwa fiye da farashin da doka ta amince zasu rufeshi.
Amma dillalan man fetur din sun kira taron manema labarai inda suka bayyana dalilin sayar da man fiye da farashin gwamnati. Alhaji Muhammad Usman Dodo sakataren kudi da kungiyar a yankin arewa ta tsakiyar Najeriya yace su ma sun sayi man ne da tsada kuma ba zasu sayar su fadi ba.
Kungiyar tace zata bi doka. Zasu bude gidajen man su sayar yadda aka ce su yi hasara amma bayan sun gama sayarwa zasu rufe sai ranar da suka samu man gwamnati.
Yanzu dai ana samun dogayen layi a gidajen man dake sayarwa akan farashen gwamnati.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5