Wannan ce ta sa hukumar bada agajin gaggawa ta babban birnin tarayyar Najeriya wato Abuja ta shiga aikin raba magungunan zazzabin cizon sauro a dukkanin sansanonin ‘yan gudun hijira guda talatin da suke a Abujar.
Kimanin dukkan ‘yan gudun hijira sama da dubu goma sha biyar ne za su amfana da wannan tsarin bada magunguna don kare su daga sharrin wannan zazzabin na cizon sauro. Kamar yadda shugaban hukumar agajin gaggawar Alhaji Abbas Idris ya bayyana.
Ishiyaku John da da wani Simon daga garin Gwoza sun nuna godiyarsu ga hukumar gamae da wannan daukin da ta kawo musu. To sai dai har yanzu suna da sauran korafi kamar yadda shugabar mata a sansanin yan gudun hijirar ta bayyana.
Charity Paul tace suna kara rokon samun karin yalwar magungunan da yake neman ya kasa isarsu. Musamman ma kamar yadda tace ga mata masu juna biyu wadanda yawanci idan an gwada su ake nun aba ma su da isashshen jinin jiki sakamakon zazzabin na cizon sauro.
Your browser doesn’t support HTML5