Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya, reshen ta dake jahar Nija dake arewacin Najeriya, ta karyata rahoton da jaridar Daily Trust ta buga cewa ta fara raba tallafin Naira milyan 30, da hukumomin jahar suka bayar, a zaman tallafi ga mutanen garin Suleja, wadanda bala’in ambaliyar ruwa ta afkawa makon jiya. Ambaliyar ta halaka rayuka da dukiya mai yawa.
Da yake karyata labarin, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Nija, Alhaji Ibrahim Inga, yace har yanzu suna dakon ma’aikatar kudi ta jahar ta saki kudaden. Yace kada jama’a suyi fargabar ko za’a zalunce su a rabon tallafin da gwamnati ta bayar. Yace hukumar sa a shirye take wajen ganin kowa ya sami abunda ka’ida ta nuna zata ko zai samu.
Daya daga cikin wadanda wannan bala’i ta shafa matuka, shine Malam Sa’adu Abubakar, wanda ya rasa matansa biyu da ‘yayansa su 6 a bala’in.
Jaridar Daily Trust wacce ake bugawa ko wace rana, ta wallafa labarin cewa an baiwa Sa’ad Abubakar Naira Milyan 4 da dubu dari biyu.
Da yake magana da wakilin Sashen Hausa a Minna Mustapha Nasiru Batsari, Sa’adu yace shi abunda ya shiga hanunsa shine Naira dubu dari biyu ne (200,000) zuwa yanzu.
Kokarin wakilin Sashen Hausa domin jin inda jaridar ta sami wannan labari ya faskara, domin wakilin Jaridar a Jahar Nija bai dauki wayarsa, ba duk da kiraye kirayen da Nasiru yayi, bisa umarnin shugabannin kamfanin jaridar a Abuja, wadanda suka gaya masa ya tuntubi wakilinsu dake yankin.
Your browser doesn’t support HTML5