Hukumar Abinci Ta Duniya Ta Fara Raba Agaji Ga A Kuriyar Afirka

Layin 'yan gudun hijira a wani sansani dake kasar kenya.

Hukumar abinchi ta Majalisar Dinkin Duniya ta fara rarraba agajin abinchin gaggawa ta jiragen sama a yankin dake fama da fari kudu maso gabashin Afirka.

Hukumar abinchi ta Majalisar Dinkin Duniya ta fara rarraba agajin abinchin gaggawa ta jiragen sama a yankin dake fama da fari kudu maso gabashin Afirka.

Jami’in hukumar abinchi ta Majalisar, ya shaidawa muryar Amurka a cewa lallai kam ana ci gaba da rarraba agajin kayan abinchi.

Jirgin farko na dauke da sama da ton goma sha hudu na kayan abinchi, wanda ya sauka jiya laraba a birnin Mogadishun Somaliya.

Tun Talata ya kamata a fara jigila da raraba kayan agajin abinchin , amma sai aka hadu da matsala wajen shirya yadda za’a gudanar da jigilar a kasar Kenya.