Hudson-Odoi Yana Farin Cikin Lallasa Lille OSC

Callum Hudson-Odoi

Dan wasan gaba na Chealsea Callum Hudson-Odoi ya bayyana farin cikinsa da ya taimakawa kungiyarsa tayi nasara a kan Lille OSC ta kasar Faransa, a gasar cin kopin zakarun Turai da yammacin ranar Laraba.

Dan wasan mai shekaru 18 da ya yi wasan na yammacin Laraba bayan dan rashin lafiya ya yi, shine ya jefawa William kwallon shi kuma ya saka kwallon a raga da ya kai Chelsea mai inkiya “the Blues” ga nasara da ci 2-1 a wasan da suka yi a can Faransa inda ta je bakwanci.

Hudson-Odoi ya dora a kan shafinsa tweeter, yana mai cewa, cin kopin zakarun Turai na farko, da maki uku da kuma taimakawa a saka kwallo a raga.

Dan wasan gaban Chelsae Tammy Abraham shine ya fara sakawa “the Blues” kwallo na farko.

Shima mai wasan gaba dan Najeriya mai yiwa Lille wasa ya sakawa kungiyarsa kwallo wasan na minti 11 da farawa, kafin Chealsea ta kara kwallo ta karshe.