Kungiyar rajin kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce tsoffin shugabannin mulkin sojan Mali ne ke da alhakin bacewar sojoji akalla 20 da ake zargin su na da alaka da wani yinkurin juyin mulki.
Wani rahoton wannan kugiyar mai hedikwata a birnin New York na zargin cewa Keftin Amadou Sanogo da dakarunsa sun kame jami’an tsaro 80, ciki har da sojoji 20n da su ka bace.
Keftin Sanogo da dakarunsa sun jagoranci juyin mulki a watan Maris sun kuma zargi wasu mutane 80 da yinkurin yi masu juyin mulki su ma a karshen watan Afirilu.
Bayan matukar matsin lambar kasa da kasa, Keftin Sanogo ya mika ragamar mulki ga wata gwamnatin wuccin gadi. To amman al’ummar duniya ta ce ya cigaba da yin katsalandan cikin harkokin gwamnati.
Kungiyar Human Rights Watch ta ce Corrina Dufka ya ce dakarun da ke goyon bayan Sanogo sun gallaza wa wadanda su ke ganin su na adawa da su a sansanonin soji biyu.
Rahoton na Human Rights Watch gabatar da hujjoji daga shaidun da su ka ce kuntatawar ta hada duka mai tsanani, da shakewa, da fyade, da hada abinci da ruwa da kuma kona wa mutum sigari a jiki.