Tsohon Shugaban Masar Hosni Mubarak, Ya Rasu, Yana Mai Shekara 91
Mubarak wanda ya taka rawa wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya aka kuma hambarar da gwamnatinsa a guguwar sauyin da ta ratsa kasashen larabawa, ya rasu ne a yau Talata.
Ya kwashe shekara 30 ya na mulkar kasar ta Masar, kuma kamar sauran shugabannin kasashen larabawa, Mubarak ya mulki Masar tamkar mallakinsa.
An yi ta zargin shi da bai wa ‘yan uwansa da abokansa mukamai masu maiko tare da yunkurin sa dansa ya gaje shi.
A watan Janairun shekarar 2011, zanga zangar adawa da gwamnatin Mubarak ta barke a birnin Alqahira da sauran biranen kasar, wacce ta kai ga hambarar da shi.
Daga baya hukumomi sun tsare shi aka kuma tuhume shi da laifin kisan masu zanga zanga.
A ranar biyu ga watan Yunin shekarar 2012 kotu ta same shi da laifin gaza wa wajen kare rayukan daruruwan masu zanga zanga da suka yi bore.