Hira da Dr. Sambo Sadiku Kan Raguwar Mutuwar Kananan Yara a Nijar Kashi na Daya

Wasu kananan yara

Binciken wata cibiya mai zaman kanta da ake kira Save The Children ya nuna cewa an sami raguwar mutuwar kananan yara a Jamhuriyar Nijar.
Binciken wata cibiya mai zaman kanta da ake kira Save The Children ya nuna cewa an sami raguwar mutuwar kananan yara a Jamhuriyar Nijar.

A cikin hirarsu da wakilin Sashen Hausa Abdoulaye Maman Ahmadu, Dr. Sambo Sadiku ya bayyana cewa bisa ga binciken cibiyar Nijar ita ce kasa ta fari da aka sami raguwar mutuwar kananan yara. Yace binciken da aka yi tsakanin kasashe saba’in da biyar.

Dr Sadiku yace an kula da fannoni uku ne a wajen binciken da suka hada da rage mutuwar yara da daidaitawa tsakanin talaka da mai kudi da kuma mace da namiji. Yace bisa kan wadannan ne aka yi bincike aka kuma gani cewa Nijar ita ce kan gaba. Dalili kuwa inji Dr Sadiku shine tunda aka yi muradun karni, Nijar ta maida hankali kan cimma na hudu wanda yake maida hankali a kan rage mutuwar kananan yara.

Dr. Sadiku yace daga shekarar alib dari tara da tasa’in an taso ana samun mutuwar kananan yara dari uku da goma sha takwas bisa kan yaro dubu suke mutuwa a Nijar, saboda haka suka ce ya kamata a rage mutuwar yaran nan zuwa kashi biyu cikin uku kafin alib dubu biyu da goma sha biyar. Yace yanzu a shekara ta dubu biyu da goma sha uku an sami raguwar mutuwar kananan yara daga dari uku da goma sha takwas zuwa dari da goma sha bakwai. Wani binciken kuma ya nuna cewa kananan yaran da suke mutuwar dari da goma sha bakwai ne. Wannan ya nuna cewa Nijar ta cika burin da ta kayyade kafin lokacin ya yi ta kuma zama kasa ta daya da ta cimma wannan burin.

Ga Kashi na farko na hirar Dr. Sambo Sadiku da Abdoulaye Mamman Ahmad.

Your browser doesn’t support HTML5

Hira da Dr Sambo Sadiku