Hira Da Dr. Sambo Sadiku Kan Raguwar Mutuwar Kananan Yara A Nijar Kashi Na Biyu

Wasu kananan yara

A ci gaba da bayanin Dr Sambo Sadiku kan raguwar mutuwar kananan yara a jamhuriyar Nijar a cikin hirar su da wakilin sashen Hausa Abdoulaye Mamman Ahmadu.
A ci gaba da bayanin Dr Sambo Sadiku kan raguwar mutuwar kananan yara a jamhuriyar Nijar a cikin hirar su da wakilin sashen Hausa Abdoulaye Mamman Ahmadu.

Dr Sadiku yace, dangane da mutuwar kananan yara, an samu rata tsakanin talaka da masu kudi, ko yan kauye da yan birni, an samu tangarda kadan. Ya ce, anan, ba samu dari bisa dari ba.

Dr Sadiku ya kara da cewa a cikin binciken su, sun game cewa a cikin kananan yara, yara maza sun fi mutuwa. Ya bayana cewa dalilin da ya sa maza sun fi mutuwa shine domin mata sun fi samun kula ta wajen uwayen su fiye da mata, musaman domin yara maza suna yawan yawo suna wasa da harkar su.

Ya kuma ce abin da ya sa jamhuriyar Nijar take samun cigaba wajen rage yawan mutuwar yara shine domin ayukan da masu kula da lafiya suke yi domin kawas da wanan matsalar. Ko da shike Nijar tana baya a talauci da mace macen mata da sauransu, Dr Sadiku yace suna yin iyakan kokarinsu su gani menene yake kashe kananan yara kuma menene zasu iya yi domin rage wanan damuwar.

Your browser doesn’t support HTML5

Hira da Dr Sambo Sadiku 2