Hillary Clinton Tana Yiwa Kwamitin Majalisar Amurka Bayani

Hillary Clinton tana isa majalisar dokokin Amurka domin yin bayani. Washington, D.C., Oct. 22, 2015

Yanzu haka tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta soma gabatarda bayanai a gaban wani kwamitin musamman na ‘yanmajalisar dokokin Amurka.

Kwamitin da akace ‘yan jam’iyyar dake adawa da ita ta Republicans ne ke da rinjaye akansa, wanda kuma yake gudanarda bincike akan harin da aka kai akan opishin jakadancin Amurka a birnin Benghazin Libya a shekarar 2012.

Ana sa ran Ms. Clinton zata wuni tana bada bayanai masu yawa dangane da wannan farmakin da aka kai ran 11 ga watan Satumban 2012 din,inda a ciki aka kashe tsohon jakadan Amurka Christopher Stevens da wasu Amurkawa guda ukku – kuma wannan ta faru ne a lokacinda ita Hilary Clinton take kan mukamin Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka.

Sai dai Ms. Clinton tana bayyana a gaban majalisar dokokin ne a daidai lokacinda ake ta zargin ‘yan jam’iyyar ta Republicans akan cewa sun suna anfani da wannan bincike ne don kawo cikas ga kokarin da Ms Clinton ke yi na zama ‘yar takarar shugaban kasa ta jam’iyyar Democrats a zaben 2016.