Hillary Clinton Ta Na Samun Lafiya Sosai Daga Ciwon Hakarkari

Hillary Clinton

Likitar yar takarar shugaban kasa a jami’iyar Democrat Hillary Clinton tace Hillary din tana samun lafiya sosai daga ciwon hakarkari da ya cafke ta kuma tana jin karfin jiki da zata iya jan ragamar shugabancin Amurka.

A wata wasika kwamitin kampen na Clinton ya fitar jiya Laraba, likitanta Lisa Bardack tace an yiwa yar takarar Democrat din gwajin kirji kuma an gano cewa ta sami bugun kwayar cutar hakarkarin ne, to amma a cewar Likitar, Hillary Clinton tana samun lafiya sosai a dalilin magungunnan da aka bata, tana sha, tare da dan hutun da take samu.

A yau Alhamis ne Clinton zata koma yawon kampen nata. Rashin lafiyarta ya zama abin magana ne bayanda aka ganta tana nuna alamun samun jiri, kamar zata fadi, jim kadan bayan da ta baro wurin da ake shagalin tuna farmakin tara ga watan Satumban da aka kai a New York shekaru 15 da suka wuce, inda har wani hoton video ya nuna tana zamewa kamar zata fadi, lokacinda take kokarin shiga mota.

Wannan al’amari ya ya dada janyo hankalin jama’a da abokin karawarta na Republican Donald Trump wanda ke yawan sukar lamirin cewa shin Clinton tana da kwarin da zata iya shugaban kasar Amurka?

Shi kuma a nashi gefen, DonaldTrump yace shi ma kamar kowane dan Amurka ne, yana so ya rage nauyi ne kawai.

Trump ya shaidawa Dr. Mehmet Oz mai gabatar da wani shirin lafiya na telbijin a jiya Laraba cewa yana so rage nauyinsa daga kilograma 7 zuwa 9.