Tsohon dan wasa kungiyar Arsenal, Thierry Henry ya bayyana cewa har yanzu yana da sha'awar zama kocin kungiyar, wanda ake ganin ya taka muhimiyyar rawa a shekarar 2018 bayan ficewar Arsene Wenger.
Henry ya buga wa Gunners wasa tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, ya taimaka wa kungiyar ta lashe manyan kofuna guda shida gaba daya, gami da lashe kofuna biyu na Firimiya Lig, kafin komawarsa na kankanin lokaci a matsayin aro a shekarar 2012.
Dan wasan da ya lashe kofin Duniya, ya zura kwallaye 228 cikin wasanni 376 da ya buga a Arsenal, kuma ya zamo dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a raga, kana ana daukar shi a matsayin dan wasa da yafi ko wane a tarihin kungiyar.
Rahotanni sun ce Arsenal ta yi wa Henry tambayoyi game da matsayin kocin kungiyar kafin nada Unai Emery, don maye gurbin Wenger shekaru biyu da suka gabata, bayan nasarar da ba faranshen ya samu a matsayin mataimakin Roberto Martinez na tawagar kasar Belgium.
Henry ya kammala aikinsa na mai horarwa a kungiyar Monaco, amma ya dauki tsawon watanni uku kacal, yana jagorantar kungiyar bayan ya yi nasarar lashe wasanni hudu daga wasanni 20 da ya yi.