Birgediya Janar John Agim, kakakin hedkwatar sojojin Najeriya, ya ce yayinda gwamnatin Amurka ta amince da sayar wa kasar makamai, abun da bata yi ba can baya, sai gashi kungiyar Amnesty na kakale kakalen neman laifin sojojin kasar domin Amurka ta fasa sayar wa Najeriya makaman.
Kakakin ya bada misali, yace a shekarun 2013 zuwa 2014 Amnesty ta ayyana cewa sojojin Najeriya na take hakkin bi’l Adama, abun da ya sa Amurka ta ki sayar wa kasar makamai a shekarun baya. Kazalika cikin wannan shekarar da Amurka ta yarda ta sayar wa kasar makamai sai ga kungiyar fara fitar da rahotanni batanci iri-iri kusan kowani wata a kan Najeriya.
A cewar kakakin abun da Amnesty ke so shi ne kasar ta ci gaba da kasancewa cikin rikici da tashin hankali. Ya zargi Amnesty da kin jin ta bakin sojojin, sai dai sojojin su ji korafe korafen kungiyar ta kafafen yada labarai.
Amma da yake maida martani, Malam Isa Sanusi, kakakin kungiyar Amnesty a Najeriya, ya ce su basu taba cewa kada a sayarwa Najeriya makamai ba. Y ace kungiyarsu ta kare hakkin dan Adam ce, kuma tana aiki a kasashe 159. Dangane da rubuta rahotanni akan sojoji ba tare da tuntubarsu ba, Malam Isa Sanusi yace duk rahoton da zasu tara akan sojojin sai sun rubutawa rundunarsu wasika domin jin tasu bahasin, amma sojojin basu taba bada amsar koda wasika daya ba. Wajibi ne a kare farar hula, Kada a ci zarafinsa kada kuma a kuntata masa a cewar Malam Isa Sanusi.
Malam Sanusi ya ce sojoji basa son a fada masu su kiyaye da hakin dan Adam.
A saurari karin bayani a rahoton Hassan Maina Kaina
Your browser doesn’t support HTML5