Taron da sashen hulda da jama’a na sojojin Najeriya ya jagoranta, an shirya shi ne da zummar kara fahimtar juna tsakanin sojoji da ‘yan jarida.
An tattauna irin rawar da sojoji ke takawa wajen samar da tsaro cikin kasar da kuma abubuwan da suka shafi hakin DanAdam.
Kungiyoyin dake fafutikar kare hakin bil Adama sun sha sukan lamirin sojojin bisa zargin take hakin mutane.
Kakakin hedkwatar sojojin Najeriya, Birgediya-Janar Sani Usman Kukasheka yace sun fi yabawa da a nemi soja su inganta yadda suke gudanar da ayyukansu, maimakon a dinga yi musu kushen ba gaira, ba dalili.
Bako mai jawabi a wurin taron, Farfesa Mande Sama’ila, ya yi wa kungiyoyin kasa wankin bargo akan yadda suke yawan sukar lamirin sojojin.
Ga Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5