Wannan dai na nuni da cewa matsin rayuwa da al’ummar Najeriya ke fuskanta ya dada muni la’akari da canjin da aka samu na hauhawar farashin kayayyaki musamman na masarufi wanda suka rubanya na shekarun baya da suka gabata
An samu kari a hauhawar farashin kayayyakin abinci, daga kashi 20.60 cikin 100 a watan Yuni zuwa kashi 22.02 a watan Yuli, wanda ake ganin ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin biredi da hatsi, da sauran kayayyakin abinci
Alkalumar farashin kayayyakin masarufi na hukumar kiddiga ta Najeriya a watan yulin shekarar 2022 da muke ciki ya yi nuni da cewa an samu karuwar kashi 18.17 cikin 100 wato sama da kashi 18.62 cikin 100 da aka samu a watan Yuni da ya gabata a shekarar lamarin da ke nuni da cewa an samu sauyin farashi a ayyuka da kayyakin da mutane ke amfani da su na yau da kullun batun da masanin tattalin arzikin kasa a Najeriya Dakta Isa Abdullahi ya ce hakan ba karamin shafar tattalin arzikin kasar zai yi ba, ta fannin tsare tsare.
A nashi bangaren, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a kasar Hassan Sardauna cewa ya yi dole al’umma su yi wa kasar adalci domin hauhawar farashin kayayyaki ya shafi kasashe da dama a fadin duniya.
Rahoton dai ya bayyana cewa an samu kari mai yawa a farashin kudin siyan iskar gas, man fetir da dizal da jigilar fasinjojin jiragen sama, tufafi, da dai sauransu
Saurari cikakken rahoton Ibrahim cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5