Jim kadan bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a Najeriya, matasa sun fito kan tituna a fadin kasar suna nuna murna da mashuna, motoci da dai sauransu wannan yasa wasu sun rasa rayukan su wasu kuma sun jikkata.
Wani matashi Dr. MK Hassan, mazauni kasar Amrka, yayi kira ga matasa da su kaurace ma irin wannan dabi’ar. Ya kara ankaradda jama’a kancewar zababben shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari, shi da kanshi yayi kira da cewar mutane su yi hankali wajen nuna jin dadinsu da wannan chanji da Allah, ya kawo musu kada su mai dashi wani abu da zai sa kasar cikin wani hali.
Kasancewar duk wanda ya zama cikin rashin lafiya to wannan haki ne na zababben shugaban kasa ya sama musu ingantantu magunguna. Don haka yayi kira da cewar don Allah matasa, da ma suaran al’umar kasa a guji aika ta duk wani abu da zai iya kawo rashin fahim ta ga kasa baki daya. Yace nuna farinciki abu ne me kyau, yaka mata ayi to amma ayi shi yadda ba zai sa kasar cikin halin tagumi ba.