Wasu rahottani na cewa kamfanin sadarwa na duniyar gizo na yahoo.com, a cikin asiri, ya dauki kofin miliyoyin sakonnin email na masu anfani da shi, ya mika bayanan ga hukumomin leken asirai na Amurka – ba tare da sanin wadanda aka dauki sakonnin nasu ba.
Kamfanin dillacin labarai na Reuters, yace a shekarar da ta gabata ne kamfanin na Yahoo.com ya gudanar da wannan leken asiran bayan da ya samu umurnin yin hakan daga Hukumar Tsaro ta Kasa ko kuma Hukumar Binciken Manyan laifuka ta Amurka ta FBI.
Wasu tsofaffin ma’aikatan kamfanin yahoo sun fadawa Reuters cewa gwamnati ce ta takurawa Yahoo da ya binciki wasu hafufa da lambobi a cikin sakonnin email na mutane. Yana nunin cewa gwamnati na neman wasu takamaiman bayanai ne.
Hakan yasa kamfanin yahoo ya kirkiri wata manhaja da zata rinka bincikar sakonnin da mutanen ke aikawa kuma suna karba ba tare da saninsu ba, ta amfani da harufan da gwamnati ta umarcesu.
Kamfanin yahoo dai ya fitar da wata sanarwa yana mai cewa “shi kamfanine mai bin doka, kuma yana bin duk dokokin kasar Amurka sau da kafa.”
Wasu masana sunce wannan shine karo na farko a tarihi da aka taba samun wata kafar sadarwar da ta bayar da rokon wasu hukumomi na gwamnatin Amurka na yayi musu leken assiran dukkan sakonin mutane masu shigowa na “emails”, maimakon ta yadda aka saba na duba wasu sakonni kalilan kuma jefi-jefi.