Hattara Da Kamfunan Hada-Hadar Kudade Da Hannun Jari Na Bogi - EFCC

EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta bankado wasu kamfunan hada-hadar kudade da saka hannun jari ta yanar gizo na bogi.

Shugaban hukumar ta EFCC shiyar Sakkwato Bawa Usman Kaltungo yace hukumar ta yi dirar mikiya akan wasu masu gudanar kamfunan bugi ta yanar gizo bayan da ta sami koke daga bankin UBA akan asusun ajiyar kudi na wani kamfani da ya gudanar da hada-hadar kudi sama naira biliyan uku da miliyan dari biyar cikin watanni shida kacal.

Lokacin da hukumar ta soma bincike akan kamfanin mai suna ‘Annexation sai ta gano cewa kamfanin na bogi ne, wanda kuma aka bude asusun ajiyar kudinsa na bankin da adireshin bugi da lambibin wayoyin salula wadanda ba'a yiwa rijista ba.

Hakama hukumar ta lura da cewa mutane da yawa sunyi huldar makudan kudade da kamfanin na bugi daga sassa daban daban na Najeriya.

Kuma a cewar Kaltungo, masu wannan kamfanin suna amfani da kudaden wajen azurta kansu ta hanyar sayen filaye da manyan gidaje da motoci.

Yanzu haka dai hukumar ta kama mutum biyu masu hannu a wannan almundahanar kuma ta sami umarnin kotu na rufe asusun ajiyar kudin nasu kafin daga baya ta kammala gudanar bincike da gurfanar da mutanen a gaban kuliya.

Akan haka hukumar tayi Kira ga jama'a da su daina yarda da duk kamfanin da zai tunkare su da sunan su bayar da kudi a ninka musu adadinsu cikin kankanen lokaci.

Haka kuma ta gargadi jama'a da su rika bincike kan sahihancin kamfani da hanyar neman sanin ko yana da rijista da hukuma kafin suyi huldar kudi da shi.

Kalli hira da Shugaban hukumar ta EFCC shiyar Sakkwato kan kamfunan hada-hadar kudade na bogi:

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban hukumar ta EFCC shiyar Sakkwato kan gano wasu kamfunan hada-hadar kudade na bogi