Ofishin Friministan Kamaru ya tabbatar da aukuwar hatsarin jirgin sama na kamfanin Laronet na masu jigilan ma’aikatan kamfanin Cotco, masu sanya bututun man fetur tsakanin kasar Kamaru da kasar Chadi.
Hatsarin dai ya auku ne a tsakanin birnin Yaoundé da kauyen Belabo da ke jihar tsakiya, kilometa 150 tsakanin kauyen da birnin Yaoundé.
A hirarsa da Muryar Amurka, mai magana da yawun Firiministan Kamaru, Alh Sidiki Anda, ya ce wannan jirgin sama yana aiki ne wajen diban ma'ikata daga birnin Kirbi zuwa wajen matatan mai da ke garin Belabo.
Hatsarin ya faru ne a cikin dajin kauyen Nagayeboko. Mutanen da suke ciki duk sun rasu, kuma gwamnati ta na kokari ta binciki dalilin hatsarin.
Ministan sufuri tare da sauran jami'an gwamnati, ciki har da ma’iakatan kamfanin Cotco, duk sun halarci wurin hatsarin. A halin yanzu dai jami’an tsaro da na kwana kwana suna kokarin gano gawarwakin.
Saurari rahoton Mahama Awal Garba:
Your browser doesn’t support HTML5