A kalla mutane goma sha biyar cikin kimanin mutane hamsin suka hallaka a sanadiyyar hatsarin wani jirgin ruwa da ya kife da su yayin da suke tafiya cikin kogin Zamare, dake tsakanin jihar Neja da jihar Kebbi.
Shugaban karamar hukumar Agwara, Alhaji Jafaru Muhammed, wanda lamarin ya faru a yankin sa ya bayyana cewa akasarin wadanda lamarin ya rutsa da su, sun fito ne daga yankin masarautar Kwantagora ta jihar Neja, a hanyar su ta zuwa ziyarar wani dutse dake cikin ruwa da aka sami rubutun Muhammadiyya a jikinsa.
Da yake bayani a hirarsu da wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, ta wayar salula Alhaji Jafaru, ya bayyana cewa jama’a na tururuwa zuwa ganin wani dutse da aka ce anga rubutun Muhammadiyya a jikinsa, domin neman tabaraki, ya kuma kara da cewa Allah kadai ya san yawan adadin jama’ar da lamarin ya rutsa da su tunda akasi baki ne.
Kawo yanzu dai shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja, Alhaji Ibrahim Inga, ya tabbatar da cewa an sami gawawwakin mutane goma sha biyar a asibitin Yawuri, Amma akwai sauran mutane uku da ba’a gani ba, kuma duk sauran jama’ar da suka tsira sun koma gidajensu.
Matsalar hatsarin jirgin ruwan kwale kwale na kara ta’azzara musamman a jihar Neja, lamarin da jawo asarar rayuka da dama.
Dr Isa Adamu, na jami’ar IBB, wanda ke sharhi akan al’amurra ya ce a yanzu ya zama tilas ukumomi su dauki mataki a kan wannan matsalar, domin yawancin jiragen basu da lafiya, makwanni biyu da suka gabata ne aka sami wani hatsarin da ya yi sanadiyyar rayuka da dama.
Domin Karin bayani ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Minna.
Your browser doesn’t support HTML5