Hasashen Masana Kan Jihohin Da Ka Iya Ba Jam'iyya Nasara

Dandazon magoa bayan wata jam'iyyar siyasa a Najeriya, ranar 12 ga watan Fabraru, 2019.

Yayin da Najeriya ke gudanar da babban zabenta da ya hada da na shugaban kasa da na ‘yan majalisu, masana na tsokaci kan yadda wannan zabe zai kaya, musamman tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar.

A cewar masana irinsu Dr. Usman Muhammad, akwai wasu jihohi da idan dan takarar shugaban kasa ya lashe su, za a iya cewa ya dauki hanyar lashe wannan zaben, musamman ma idan ya kalato daga sauran jihohin kasar.

“Wannan al’amari sai Allah, amma bisa kididdiga da aka samu, akwai jihohi da idan suka samu galaba akansu, kamar sun samu nasara ne a zaben, sai dai su kalato wasu jihohi haka wadanda ba a rasa ba.” Inji Dr. Muhammad.

Ya kara cewa, “jihohin nan sune Kano, Kano tana da jimillar kuri’u miliyan 5.4, Kaduna tana da miliyan 3.9 Legas tana da miliyan 6.5, to ka ga duk jam’iyyar da ta samu galaba ko da na miliyan uku-uku ne a wadannan jihohi, lallai babu shakka ta kama hanyar neman lashe zabe.”

A cewar Dr. Muhammad, sun samu alkaluman wadannda jihohi ne daga hukumar zabe ta INEC.

Saurari cikakkiyar hirar da Mhyamud Lalo ya yi da Dr. Usman Muhammad:

Your browser doesn’t support HTML5

Hasashen Masana Kan Jihohin Da Za Su Iya Ba Jam'iyya Nasara - 5'36"