Haruna Maja: Muna Yaki Da Ta'ammali Da Miyagun Kwayoyi

Yawan shaye-shayen kwayoyi da kuma bangar siyasa da matasa ke yi, ya sa muyi yaki da shaye shayen kwayoyi a ungunaninmu. Shi kuma ya sa muka kafa kungiyar Al’faida, domin kawar da wadannan matsaloli, a cewar matashi Haruna Dalha Maja, wanda aka fi sani da Haruna Maja.

Ya ce, kafin su fara wannan yaki da suke yi a yanzu, unguwanin da ke kewaye da karamar hukumar Dala, kamar su Bakin ruwa, Marmara, Jakara da sauran unguwanni, 'yan siyasa kan yi amfani da wadannan matasa masu shaye-shaye domin su zame musu 'yan bangar siyasa.

Yawancin matasa, mussaman daga unguwa zuwa unguwa, sukan yi rikice-rikice na harkar ta kwayar dan ya kara musu karfi. Ya ce, mussaman ma a yanzu da suke yin kokarin magance matsalar, sai kuma ga kakar siyasa ta doso kai. Ya lura da cewar wasu daga cikin matasan sun fara komawa ruwa.

Haruna Maja, ya bayyana cewa a baya, duk lokacin zabe, a lokkutan ne ake yawan samun masu shaye-shayen amma da yawaitar fadakarwa, wannan matsalar ta kau, sai 'yan kalilan da ba za a rasa ba.

Hukumomin da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi, na mara musu baya wajen wannan kudiri nasu, duk da cewar mafi tsaurin hukuncin da akan yanke musu, baya wuce a ci su tara, kuma yana alfahari a yanzu matasa sun farga, kuma an samu raguwar 'yan daba da bangar siyasa a tsakanin matasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Yaki Da Matasa Mashayen Kwayoyi Masu Bangar Siyasa