Harshen Turanci Na Taimakawa Wajen Yada Al'adar Hausawa

Kabiru Musa Jammaje

Wani sabon Fim mai suna 'In Search of a King' labari ne na wani yaro da yake yawo wasu garuruwa, domin ya yada ilimin Boko ga al’ummar yankunan da ya tarar, amma ya fuskanci wasu 'yan kalubale na rashin son ilimi a gari na farko, a gari na biyu kuma aka kulla masa sharri kamar yadda furodosan fim din Kabiru Musa Jammaje, ya bamu a takaice.

Mashiryen fim din ya ce ya zabi harshen Turanci ne domin ya tallata al'adar Bahaushe, tare da nuna al'adun Hausawa ta hanyar fim amma da harshen Turanci.

Jammaje ya ce duniya ta amince da cewar harshen Turanci harshe ne da duniya ta amince da shi, kuma duk duniya ake amfani da harshen, akan haka ne yaga cewar yana da matukar alfanun fitar da fim da harshen Turanci, kamar yadda takwarorinsu na 'yan Nollywood ke fina-finai da Turanci ta hanyar nuna al’adunsu ga duniya.

Ya kara da cewa ya fito da wani sabon salo na cewar mutane 2000 na farko da zasu fara kallon fim din, zasu samu kyautar littafin da babu shi a kasuwa sai ga wadanda suka je sinima domin su kalli fim din, da zummar samun wasu nazari a kan harshen Turanci.

Ya ce an kashe sama na naira miliyan biyar wajen samar da fim din, sannan an shafe watannin 6 ana daukar fim din tare da tace wadanda zasu fito a fim din 'In search of a King’ da jigonsa ya fi maida hankali ne ga yada ilimi game da nuna muhimmacin ilimi ga dukkanin al’umma.

Kabiru Jammaje ya ce ya samu alfanu da dama idan akayi la’akari da fim din da yake fitarwa da harshen Turanci, da kuma irin tasirin da hakan yayi ga mutane a sassan Arewacin Najeriya da ma kasa baki daya.