Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Mauricio Pochettino, ya bayyana cewar akwai yiwuwar dan wasan gabansa Harry Kane ya kai har zuwa karshen kakar wasan nan bai murmure ba, sakamakon raunin da ya ji a wasan da suka doke Manchester City 1-0 ranar Talata da ta gabata a wasan cin kofin zakarun turai.
Kocin yace ko da yake suna fata idan likitoci sun duba rauni ya zama ba babbar matsala ba ce dan wasan zai dawo fili kafin karshen kakar.
Dan wasan Kane ya samu raunin ne a wata haduwa da sukayi da Fabian Delph dan wasan Manchester city.
A cewar Pochettino, raunin na Kane ya daga musu hankali ganin yazo lokacin da su ke kokarin karkare kakar wasa a matsayi na 3 ko kuma na 2 a gasar Firmiya lig na bana, da kuma fatansu na ganin sun kai wani mataki a gasar zakarun Turai.
Ba wannanne karo na farko da Kane ya taba samun rauninba domin a watan Janairu bana ma Kane dan Ingila ya gamu da makamancin raunin a wasansu da Manchester United.
Tottenham dai tana matsayi na hudu ni a teburinne firimiyan Ingila mako na 33 da maki 64, inda a ranar Asabar 13 gawatan nan zata karbi bakuncin Huddersfield Town, sai kuma ranar Laraba ta ziyarci Manchester City a karawa ta biyu cikin gasar zakarun Turai na bana a matakin wasan daf da na kusa da karshe.