Lamarin da ya sa kanfanoni ke kukan rashin wutan lantarki da kuma tsadar man fetur dana diesel, makamashin da ake amfani da su wajen amfanin da injinan samar da hasken wutan lantarki.
Tuni dai hukumar samar da wutar lantarkin ta kasa TCN ta alakanta rashin wutar lantarkin da matsalar da aka samu daga tashar wutar lantarki da ke Legas wanda ake kira National Grid.
A makon da ya gabata ne dai ministan kudin Najeriya Hajiya, Zainab Shamsuna Ahmed ta ce tuni gwamnati ta tsame hannun ta daga ba da tallafin wutar lantarki.
Sai dai alamu na nuna cewa matakin gwamnatin ya yi mummunan tasiri kamar yadda masu lura da al'amura ke fada.
Wani mazaunin birnin Legas Mikail Shagarda da ke unguwan Obalande ya sheda cewa suna fuskantar matsalar wutar lantarki tun a farkon shekaran nan kuma su masu kananan sana'o'i matsalar ta fi yi wa illa, ga matsalar wutar lantarki ga ta man fetur duk sun sanya wasu ma dakatar da ayyukan su.
Dr. Dauda Mohammed Kontagora wani masanin tattalin arziki ne a kasar, wanda kuma ya ce - hakan na dakushe ci gaban kasa ta hanyar karya masana' antu da haifar da rashin aikin yi a tsakanin matasa.
Masanin ya ce babu kasar da za ta ci gaba ba tare da makamashi ba, don haka akwai bukatar gwamnati ta tashi tsaye wajen samar da shi domin raya kasa.
Yanzu dai a yayin da gwamnati da kamfanonin samar da wutar lartarki ke kokarin ganin an samar da ita a kasa, fatan 'yan Najeriya shi ne na kawo karshen karancin kamar dai sauran kasashen duniya baki daya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5