Harkar Tsaro a Shekarar Buhari Ta Farko

Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Janar Tukur Buratai, yana duba fareti a lokacin kaddamar da baburan da sojoji za su rika shiga daji da su wajen yakar 'yan Boko Haram

Matsalar tsaro na daya daga cikin batutu8wan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi alkawarin zai magance, musamman a yankin arewa maso gabashin aasar da ke fama da matsalar Boko Haram.

Tun bayan da ya lashe zabe a bara shugaba Buhari ya maida hedkwatar ba da umurni a fannin tsaro zuwa arewa maso gabas, a wani mataki na tunkarar matsalar.

Masu lura da al’amura da dama sun nun cewa an samu sauki matuka dangane da yakin da ake yi da ‘yan kungiyar Boko Haram, musamman idan aka kwatanta da yadda su ke cin karensu ba babbaka a baya.

Matsalar Boko Haram wacce aka kwashe fiye da shekara shida ana fama da ita, ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu biyu, kana wasu miliyoyin sun bar muhallansu.

Ayyukan kungiyar a shekarun baya sun fadada har sun kai ga wasu kasashe da ke makwabtaka da Najeriyra kamar su Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi.

Baya ga batun Boko Haram Najeriyar har ila yau tana fama da matsalar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

To ko yaya fannin na tsaro ya ke shekara guda bayan hawan Buhari mulki? Saurari rahoton wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina da ya aiko daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Harkar Tsaro a Shekarar Buhari Ta Farko - '5:03"