Wasu rokoki guda hudu da aka harba sun dira kan wani sansanin soja da gamayyar dakarun da Amurka ke jagoranta ke amfani da shi a kudu da birnin Bagadaza ranar Juma’a 24 ga watan Yuli, kuma rokokin sun yi barna amma ba a samu hasarar rai ba, a cewar wata sanarwar daga rundunar Sojin Iraqi.
Rokokin sun taba sansanin Besmaya, inda aka girke dakarun kasar Spain don fadan da suke yi da mayakan IS wanda Amurka ke jagoranta. Amma gamayyar dakarun na rage yawan mayakanta a Iraqi.
A cikin ‘yan watannin da suka gabata, an kai wasu hare-haren rokoki da suka taba sansanonin da aka tsugunnar da dakarun hadin gwiwar, suka kuma dira a kusa da ofishin jakadancin Amurka a Bagadaza. Amurka ta dora laifin hare-haren kan kungiyoyin mayakan da Iran ke goyon baya.
Ya zuwa yanzu dai babu kungiyar mayakan da Iran ke mara wa baya da ta dauki alhakin hare-haren.