A kalla wadannan kananan rokokin ukku ne aka harba kusa da harabar fadar shugaban kasar. Kamar yadda direban motar daukar mara sa lafiya ya shaidawa Muryar Amurka, cewa an harba rokar ne a kusa da wani gida a yankin gundumar Wardhigley dake dab da fadar shugaban kasa, kuma farar hula hudu suka samu rauni kuma an kai su asibiti.
Sai dai rahotannin sun tabbatar cewa ba ko mutun guda daga cikin ‘yan majilisar zartaswa da wannan harin ya shafa.
An dai kai wannan harin ne sa'ilin da Firayin Minista Hassan Ali Khaire, ke tattaunawa da sabbin jami'an sabuwar gwamnati kuma babba ajandar taron ita ce yadda zasu inganta matakan tsaro a kasar da kuma yadda zasu tunkari batun fari.
Sai dai kawo yanzu ba wani wanda ya dauki alhakin aikata wannan danyen aikin.Sai dai sau tari 'yan tawayen Al-shabab, sun sha kai wa gwamnati hari.