Harin Rokoki Kan Fadar Shugaban Kasar Yemel, Ya Halaka Mutane Da Jikkata Shugaba Ali Saleh

Masu zanga zangar nuna kin jinin gwamnati suke dauke gawarwakin magoya bayan sheikh Sadeq da aka kashe a fada da jami'an tsaro.

Gwamna Dankwambo ya bayyana haka ne a hirarsa ta farko da manema labarai,inda yace matsalar matsan yana damun jama'ar jihar.

Shugaban Yemel Ali Abdullah Saleh yana zargin wadan da ya kira “bata-gari” kan harin rokoki da aka kai kan fadarsa har ya halaka mutane bakwai,ya jikkata shi.

Tashar talabijin ta kasar ta watsa jawabinsa da yayi ta sauti kawai, babu hoton vidiyo, sa’o’I bayan harin rokoki da aka kai kan fadan shugaban kasar dake babban birnin kasar San’a.

Mr. Saleh yace yana cikin koshin lafiya. Amma ya tabbatar da mutuwar mutane bakwai a farmakin da aka kai. Tunda farko,wata kafar yada labaran kasar,tace an kashe dogarawan shugaban kasar su uku,san nan an jikkata liman.

Kafofin yada labaran kasashe yammacin Duniya, sun ambaci wani dan hamayya yana cewa Mr. Saleh da wasu jami’ai suna sallah cikin wani masallaci dake cikin fadar shugaban kasa,lokacinda aka kai harin.

Fadar White House tayi Allah wadai ganin karuwar tarzoma a Yemel. Haka a sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar,Amurka tayi kira da akawo karshen bata kashi da ake yi,kuma a aiwatar da shirin sulhu d a kasashe dake yankin Gulf suka gabatar,wanda daya dagsa cikin sharuddansa shine,neman ganin shuga Abdullah Saleh yayi murabus.