Harin Mulai Ya Jawo Asarar Rayuka a Kalla 15

Mutane sunyi dafifi kewaye da inda boma-boman ya tashi a Maiduguri a ranar 14 ga watan Maris 2014.

​Jami’an Najeriya sunce hare-haren kunar bakin wake a kusa da birnin Maiduguri dake arewacin kasar sun kashe a kalla mutane 15, sannan sunji wa sojoji 5 munanan raunuka.
Hare-haren na jiya Talata sun kunshi motoci 4 dake shake da boma-bomai. Jami’ai sunce motoci biyu ne suka yi karo da inda sojoji ke binciken ababen hawa, sannan bom-bom din suka far-fashe.

Jami’an tsaro sun harbe ragowar direbobin motocin guda biyu kafin su fasa nasu boma-boman.

Kwamishinan ‘yan sanda jihar Borno yace wannan harin yana kama da na kungiyar tada kayar baya ta Boko Haram.

An dai dorawa kungiyar alhakin kashe dubban mutane tun shekara ta 2009. Kungiyar Amnesty International ran litinin dinnan tace mutane 1,500 ne suka mutu a tarzoma dake da alaqa da Boko Haram a wannan shekarar.