Harin Makarfi

  • Ibrahim Garba

Saboda yanayin tsaro yanzu an fai ganin sojoji a sassan Nijeriya

Har yanzu ba a tantance ko su wa su ka kai hari garin Makarfi da daren Lahadi ba. Wasu na ganin 'yan fashi ne; wasu kuma na ganin 'yan Boko Haram ne.
Wasu ‘yan bindigar da ba a tantance ko su waye ba sun kai hari garin Makarfi na jihar Kaduna da daren jiya Lahadi da misalin karfe takwas zuwa takwas da rabi na daren.
Wakilinmu na garin Kaduna, Isah Lawal Ikarah ya ce yayin da wasu ke ganin maaharan ‘yan fashi da makami ne akwai wasu kuma da ke ganin ‘yan kungiyar Jama’atu Ahlis-
Sunnan Lid Daawati wal Jihad ne da ake wa lakabi da Boko Haram.

Wani ganau ya gaya ma wakilinmu na jihar Kadunan cewa isarsu garin Makarfin ke da wuya sai maharan su ka dira kan ofishin ‘yan sandan garin, inda su ka yi ta harbe harbe. Daga nan kuma su ka wuce bankin garin, inda su ka kwashe kimanin sa’o’I su na ta harbe harbe har da tayar da abubuwan da ake ganin bama-bamai ne; su ka yi kaca kaca da shi. Y ace al’amarin ya yi kama da wanda ya faru kwanan baya a Saminaka.

Wakilin na mu ya ce kodayake lokacin da maharan ke harbin suna ta cewa “Allahu Akbar!” wasu na ganin harin bai da nasaba da kungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lid Daawati wal Jihad da ake wa lakabi da Boko Haram. Y ace shi kansa Gwamnan jiahr Kaduna, Alhaji Mukhtari Lamaran Yero da ya kai ziyara wurin y ace lallai harin ya yi kama da fashin da aka taba kai wa Saminaka kwanan baya. Wakilin namu ya ce wani dan garin kuma ganau ya shaida masa cewa maharin bas u harbi wani dan garin ba. To amma wakilin na mu y ace kwamishinan ‘yan sanda y ace har yanzu ana binciken abin da ya faru a ofishin ‘yan sandan.

Your browser doesn’t support HTML5

Harin Makarfi - 2:45