Wani harin kunar bakin wake da 'yan Taliban su ka kai da mota ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 35 baya ga wasu da dama da su ka jikkata a Kabul babban birnin kasar ta Afghanistan.
Wani mai magana da yawun Ma'aikatar Cikin Gida Najib Danish, yayin da ya ke tabbatar da adadin wadanda abin ya rutsa da su, ya yi bayanin cewa maharin ya gwabje motarsa da ke shake da bama bamai cikin wata mota mai dauke da ma'aikatan gwamnati farar hula a sashin yamma na birnin.
Fashewar ta auku ne yayin da motar bus din ke ratsa wata cinkusasshiyar kasuwa, inda ta rutsa da masu kantuna da masu wucewa, a cewar wasu ganau.
Jami'an asibiti na kyautata zaton adadin wadanda abin ya rutsa da su zai karu.
Wani mai magana da yuwan rundunar 'yan sanda ya gaya ma Muryar Amurka cewa wadanda abin ya rutsa da su akasari ma'aikatan kamfanonin mai ne da na hakar ma'adanai.