Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutane 13 Ya Jikata 85 A Pakistan

Wurin da aka kai harin kunar bakin wake a Lahore, Pakistan

'Yansanda da shaidu a Pakistan sun ce wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a wajen wani zanga-zanga, a birnin Lahore da ke gabashin kasar, wanda ya hallaka mutane akalla 13 ya kuma raunata wasu 85.

Wasu manyan jami'an 'yansanda biyu na cikin wadanda su ka mutun kuma masu ayyukan ceto na fargabar yiwuwar adadin mace-macen ya karu.

Wasu masu sana'ar harhada magunguna ne su ka shirya zanga-zangar don nuna adawarsu da wasu sabbin dokoki.

Shaidu sun ce 'yansandan da su ka mutun na kokarin daidaitawa ne da masu zanga-zangar don kawo karshen gangamin lokacin da bam din ya tashi.

Wani da ya jikata a harin

Wani reshen kungiyar Taliban shiyyar Pakistan wanda ya balle, ya yi ikirarin kai wannan harin, wanda ya auku a hedikwatar lardin Punjab, wanda ya fi yawan jama'a a kasar. Wani mai magana da yawun kungiyar Jamaat-ul-Ahrar ya ce daya daga cikin 'yan kunar bakin wakensu ne ya kai harin.