Wani harin kunar bakin harin kunar bakin wake biyu da mayakan Boko Haram suka kai da safiyar yau Asabar a Maiduguri fadar jahar Borno, ya halaka akalla mutane 9 da jikkata wasu 24, a jahar da ta kasance cibiyar tada kayar bayan da 'yan bindigar suke ta yi na tsawon shekaru bakwai yanzu.
Rundunar sojojin Najeriya tace daya daga cikin bama-baman ya tashi ne a kofar wani sansanin da 'yan gudun hijira fiye da dubu 16 suke, wadanda rikicin 'yan binidgar ta raba da muhallansu tun asali. Bam na biyu ya tashi ne harabar gidan mai mallakar gwamnati.
Nan da nan dai babu wanda ya dauki alhakin kai wannan hari, amma bama-bama sun kamada irin aika-aikar da Boko Haram ta aiwatar a baya.
A baya bayan kungiyar ta zafa-zafa kai hare hare bayan lafawa na watanni sakamkon rigimar shugabanci tsakanin 'yan kungiyar.
Asusun kula da yara ta MDD UNICEF tayi kiyasin yara kimanin dubu 50 ne suka fuskanatar kasadar 'yunwa zata kashe su mudddin basu sami abinci ba,yayinda wasu dubu metan da hamsin tuni suke fama da katancin abinci mai gina jiki.
Koda yake shugaban Najerya Muhammadu Buhari ya yi nasarar daukar matakan soji da yayi nasara kan kungiuyar tun bayan da ya kama aiki shekara daya data shige, har yanzu Boko Haram tana kai munanan farmaki.
Kuma fitinar yanzu ta bazu zuwa kasashe makwabta da suka hada d a Nijar, da Cadi,da kuma kamaru.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5